1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron EU a gabanin yarjejeniyar Brexit

Abdoulaye Mamane Amadou
October 17, 2019

Kungiyar Tarayyar Turai na shirin gudanar da babban taron koli domin tattauna batun ficewar Birtaniya daga kungiyar EU a daidai lokacin da ake cikin kila wa kala kan cimma wata yarjejeniya game da batun Brexit

https://p.dw.com/p/3RQ9T
Belgium Europe Brexit  Michel Barnier
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Seco

Rahotanni sun ce tuni bangarorin da ke shiga tsakani kan batun ficewar Birtaniyar sun nuna cewa an samu muhimmin ci gaba a tattaunawar da ake, kana kuma hakan kan iya kai ga bangarorin biyu cimma wata yarjejeniya a gabanin ficewar Birtaniya daga EU.

Taron na kwanaki biyu da shugabannin za su gabatar dai na a matsayin na karshe ga Birtaniya, gabanin shirye-shiryen ballewar kasar daga kungiyar a ranar 31 ga wannan watan.

Ko baya ga batun na Brexit wata majiyar diflomasiya ta tabbatar da cewa, shugabannin za su kuma tattauna muhimman batutuwan da dama da suka shafi kungiyar, ciki har da bayyana matsaya guda kan batun luguden wutar da Turkiyya ke yi wa mayakan Kurdawa da ke kasar Siriya.