1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya na gab da barin kungiyar EU

Binta Aliyu Zurmi
January 29, 2020

Shuwagabanin hukumar zartaswa na kungiyar tarayyar Turai na shiye-shiryen karshe na jadawalin yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar.

https://p.dw.com/p/3Wziz
Von der Leyen zum Kommissions-Start
Hoto: picture-alliance/dpa/Belga/T. Roge

A kalaman su na bankwana sun gargadi Birtaniya cewa kada ta bijiro da wasu ka'idoji na son zuciya a game da sha'anin kasuwanci da sauran mambobin kungiyar ta EU.

Shugabar hukumar zartarwa ta EU Ursula von der Leyen, ta yi jawabi mai motsa zukata inda ta ce "ba zamu taba daina son ku ba kuma ba za ku yi mana nisa ba" wannan jawabi na Von der Leyen ya ratsa zukatan 'yan majalisar inda har sai da wasu daga cikin su suka zubar da hawaye.

Birtaniya dai ita ce kasa ta farko da zata fice daga kungiyar EU. A ranar Juma'ar nan da ke tafe da misalin karfe sha daya na rana za a kawo karshen batun Brexit da aka kwashe shekaru hudu ana kai ruwa rana a kansa.