1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Eritriya ta kaddamar da farmaki a Tigray

Usman Shehu Usman
September 23, 2022

Fdan da ya sake barkewa a yankin Tigray na kasar Habasha musamman a kusa da iyakar Tigray da Eritriya ya dauki hankalin jaridun Jamus a wannan makon.

https://p.dw.com/p/4HHN3
Symbolbild Pressespiegel
Hoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

Eritriya ta kaddamar da gagarumin farmaki a yankin Tigray. Wannan shi ne labarin Neue Zürcher Zeitung, Fadan dai ya biyo bayan tsagaita wutar da aka shafe watanni biyar ana yi inda ake ganin an cimma yarjejeniyar zaman lafiya bisa dukkan alamu da goyon bayan sojojin kasar Habasha da kuma mayakan sa kai na yankin. Hare-haren na nufin ruruta yakin da ya sake barkewa a karshen watan Agusta. Jaridar ta ci gaba da cewa, kakakin gwamnatin yankin Tigray, ya rubuta a shafin Twitter cewa, "Eritreya ta tattara dukkan sojojinta, ciki har da 'yan gudun hijira." An gwabza kazamin fada a kusa da iyakar Tigray da Eritriya. 

Ita kuwa jaidar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi rundunar sojan Jamus ta sake dakatar da ayyukanta a wani bangare na tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA a kasar Mali. Jaridar ta ci gaba da cewa kamar yadda wani kwamandan sojin Jamus ya fada. An katse tsarin aikin na wanzar da zaman lafiya, kuma ba a tabbatar da tsaron lafiyar sojojin ba. Dalilin hakan dai shi ne, izinin gudanar da aikin tsaron kasar ta Mali, ya kare kuma ba a sabunta shi ba. Wannan ya kamata ya sake tada muhawara game da ci gaba da aikin sojojin Jamus a Mali da ke haifar da cece-kuce.

Mittelmeer Bootsflüchtlinge aus Tunesien
Hoto: Francisco Seco/AP Photo/picture alliance

Ita kuwa jaridar die Welt ta duba kokarin dakatar da kwale-kwalen bakin haure ta yi wanda masu tsaron kan iyakokin Tarayyar Turai suke yi na hana ficewa daga Senegal.  A baya bayan nan dai Senegal na neman zama wata sabuwar hanyar da bakin haure ke bi izuwa Turai kamar kasar tsibirin Canary na kasar Spain, yana da nisan kilomita 1500 daga Dakar babban birnin kasar Senegal a kan Tekun Atlantika, amma duk da haka mutane suna gwada tsallakawa. Kimanin bakin haure 11,000 ne suka bi ta hanyar wajen shiga Turai, daga farkon bana  zuwa yanzu, ta iyakoki kama daga Morocco, Mauritania, Senegal da Gambia. Bayan hanyar tsakiyar tekun Bahar Rum zuwa Italiya, ita ce hanya mafi yawan zirga-zirga da bakin haure ke bi zuwa Tarayyar kuma ita ce mafi hatsari.

Deutschland | Schwesig und Habeck am Energiestandort Lubmin
Hoto: Stefan Sauer/dpa/picture alliance

Sai jaridar die tageszeitung wace ta fara labarinta kamar haka  Gas din Afirka don Turai. Kasashen Turai na kallon Senegal mai arzikin iskar gas a matsayin madadin Rasha. A cikin gida, wannan yana haifar da bege ga ayyuka. Kasar ta Senegal ka iya taka rawa wajen samar da iskar gas ga Jamus a nan gaba. Bisa alkaluma daban-daban, za a samar da sabbin ayyukan yi daga 150,000 zuwa 200,000 a duk shekara domin dakile rashin aikin yi yadda ya kamata. A wani bincike da aka gudanar a karshen bara, ya nuna rashin aikin yi shi ne babban matsalar da gwamnatin shugaba Macky Sall ke bukatar a magance cikin gaggawa. Ana la'akari da saka hannun jari na kasashen waje sosai.