1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Eritiriya ta ɓalle daga Ethiopiya a shekara 1993

January 7, 2013

Kamin Eritiriya ta samu ta zama ƙasa mai cikkaken 'yanci sai da ta sha gwagwarmaya da Ethiopiya

https://p.dw.com/p/17FMn
Karte Eritrea Äthiopien
Hoto: AP Graphics/DW

Da gaske ne Eritiriya daga ƙasar Ethiopiya ta ɓalle?

Har cikin yaƙin duniya na biyu a shekara 1943, Eritiriya ƙasa ce wadda ke ƙarƙashin turawan mulkin mallaka na ƙasar Italiya.Bayan yaki ta koma mallakar ƙasar Ingila kamin daga bisani ta zama wani yanki na ƙasar Ethiopiya.

A shekara 1958 Eritiriya ta shiga gwagwarmaya domin ƙwatar 'yancinta daga Ethiopiya.An girka ƙungiyoyin tawaye masu yawa, kuma dakarun ɓangarorin biyu sun fafata yaƙi wanda ya haddasa asara dubunan rayuka.Firaministan Eritiriya na yanzu Issayas Afeworki shi kansa ya jagoranci wata rundunar tawaye mai suna FPLE.

Kamar ko ina cikin duniya bayan an tafka yaƙi, kowa ya jinjina ƙarfin abokin hamayarsa, doli a koma teburin shawarwari, saboda haka bayan shekaru da dama ana yaƙe-yaƙe tsakanain dakarun aware na Eritreya da na gwamnatin Ehtiopiya, a ƙarshe dai sun koma teburin shawara bisa jagorancin ƙasar Amurika, wanda sakamakon sa gwamnatin Ethiopiya ta amince Eritreya ta shirya ƙuri'a jin ra'ayin jama'a domin ta tambaye su sun amince ko ko a'a Erithrea ta ɓalle daga Ethiopiya.An shirya wannan ƙuria'a jin ra'ayin jama'a a shekara 1991, kuma kashi 99 cikin ɗari na mutanen Eritriya suka zaɓi ɓallewa daga Ethiopiya.Bayan wannan ƙuri'a Eritreya ta samu 'yancin daga Ethiopiya ranar 28 ga watan Mayu na shekara 1993 bisa jagorancin Firaminista mai ci yanzu bugu da ƙari tsofan magudun 'yan aware wato Issayas Afeworki.To saidai kuma har bayan samun 'yancin kan ƙasashen biyu sun cigaba da zaman gaba dalili da iyakoki.

Eritrea Flagge
Tutar Eritiriya

A shekara 1998 sai da ma su ka gwabza wani yaƙi wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane kimanin dubu 70.Sannan hata yaƙin dake wakana yanzu a Somaliya tamkar wani bangare na illolin yaki tsakanin Eritreya da Ethiopiya.

Ausschnitt: Sudanese president Omar Al-Bashir, right8 nicht im Bild), and his Eritrean counterpart Isayas Afewerki, talk during their meeting in Khartoum, Sudan on Tuesday, June 12, 2006. Afewerki is on a one-day visit in Sudan. (AP Photo/Abdel Raouf)
Isaias AfewerkiHoto: AP

Yawan mutanen ƙasar Eritriya da kuma ƙasashen da ta ke iyaka da su.

Eritiriya na da yawan mutane miliyan shida.Kasar Eritreya ta na yankin kafon Afrika, ta yi iyaka da ƙasashe Sudan, Ethiopiya, Djibouti,Yemen da kuma Saudi Arabiya a iyakarta ta ruwan maliya.sai kuma babban birnin mai suna Asmara.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu