Edward Snowden ya samu takardun izini | Labarai | DW | 24.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Edward Snowden ya samu takardun izini

Wasu majjiyoyi daga Rasha na cewar hukukomin ƙasar sun ba da izinin ga tsohon jami'in leƙen asirin na Amirka da ya fice daga filin saukar jiragen sama na birnin Moscow.

Majiyoyin sun ambato jami'an tsaro na cewar jami'an shigi da fici na ƙasar ta Rasha sun bai wa Edward Snowden takardun da za su ba shi damar shiga cikin birnin Moscow.

Snowden ɗin dai ya kwashe tsawon wata guda maƙale a filin saukar jiragen sama na Mosow tun bayan da ya fice daga ƙasar Hong Gong. Sakamakon wasu bayyanai na siri na satar sauraron wayoyin jama'a da kuma karanta shafukan Intanet da hukumomin Amirka suke yi. Kuma a cikin sao'i na gaba masu zuwa zai iya ficewa daga filin saukar jiragen sama na birnin Moscow. Tun da fari dai Snowden ya ajiye buƙatar samun mafukar siyasa ga hukumomin ƙasar ta Rasha.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman