Edward Snowden ya isa Rasha | Labarai | DW | 23.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Edward Snowden ya isa Rasha

Gwamnatin Hong Kong ta tabbatar da cewar tsohon jami'in leƙen asirin Amirka ya tashi cikin jirgin sama daga ƙasar zuwa birnin Moscow.

Wani kakakin gwamnatin ya ce Snowden ya bar ƙasar ne da ƙashin kansa kuma ta hanyar ƙai'dojin da suka dace. Sannan kuma ya ƙara da cewar ba su ga wasu cikkakun hujoji na kama shi ba kamar yadda hukumomin Amirka suka buƙata a kan zargin leƙen asirin da suke yi ma shi.

A cikin watan Mayu da ya gabata ne Snowden ya isa a Hong Hong bayan da ya fallasa shirn Amirkan na sotar sauraron bayyanan wayoyin jama'a. A cikin shafinsa na sada zumunta WikiLeaks, ya ce ya taimaka wa Snowden ga samun mafuka a wata ƙasa mai bin tsarin demokraɗiyya da bai bayyana ba.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu