1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Eduardo Mondlane: Shi Ya tsare hadin kan Mozambik

Carla Fernandes
October 9, 2020

Eduardo Mondlane yana da hangen 'yanci da hadin kan Mozambik, daga Turawan mulkin mallaka na Potugal. Ko da yake an halaka shi yayin da yake gudun hijira a ketere, amma an ci gaba da manufofinsa.

https://p.dw.com/p/3jeha
African Roots  | Eduardo Mondlane

Yaushe kuma a ina aka haifi Eduardo Mondlane? Eduardo Chivambo Mondlane an haife shi 20 ga watan Yuni 1920, a Manjacaze, da ke Lardin Gaza na kudancin kasar Mozambik. Makiyayi ne har ya kai shekara 10 da haihuwa.

Me nene zurfin ilimin Eduardo Mondlane? Mondlane ya halarcin makarantar firamare ta Kirisctocin Turawan Switzerland mabiya Presbyterian kusa da Manjacaze daga bisani ya yi digiri a bangaren sanin halayyan dan Adam inda ya fara a Afirka ta Kudu ya kammala a kasar Potugal. A wajen ya gamu da shugabannin 'yan gwagwarmaya da mulkin mallaka kamar Amílcar Cabral na Guinea Bissau da Cape Verde gami da Agostinho Neto na Angola. 

African Roots  | Eduardo Mondlane

Ya kuma yi digirin digirgir a kasar Amirka. Lokacin ya bayar da darasi a jami'ar Syracuse kafin ya yi aiki a matsayin mai bincike na Majalisar Dinkin Duniya game da lamuran da suka shafi 'yancin kasashen Afirka. Daga cikin abubuwan da ya yi sun hada da taimaka wa a shirya zaben raba gardama kan makomar yankin Kamaru mai magana da harshen Ingilishi a shekarar 1961 da tantance iyaka tsakanin Kamaru da Najeriya.

Wani abu ya fito da Eduardo Mondlane aka san shi? Shi shugaba na farko wanda aka kafa kungiyar FRELIMO (Mozambican Liberation Front) a birnin Dar-es-Salam na kasar Tanzania a 1962, bayan mutuwar Mondlane kasar ta Mozambik ta samu 'yanci. An dauki Mondlane a matsayin dan juyin-juya halin kishin Afirka, da ya yi yawo kana masanin halayyan dan Adam.

Wane abu da ake tuna Eduardo Mondlane akai? Har zuwa yanzu, akwai mutanen da suka dauki Mondlane a matsayin mai nuna sanin yakamata da hada kan mutanen Mozambik bisa hangen nesa da karfafa ilimi. 

African Roots  | Eduardo Mondlane

Wane abu ya yi ajalin Eduardo Mondlane? Ranar 3 ga watan Febrairun 1969 aka kashe Mondlane a birnin Dar-es-Salam na Tanzaniya, lokacin da ya bude wasika mai dauke da bam. Wasu sun zargi masu adawa da shi a kungiyar FRELIMO da 'yan sandan sirri na Potugal bisa alhakin kisan, amma har yau lamarin ya kasance cikin duhu.

Shin Eduardo Mondlane ya rubuta wani littafi? Eduardo Mondlane ya rubuta littattafai da dama da suka hada da gwagwarmaya kan 'yancin Mozambik mai suna 'Lutar por Moçambique' da harshen Potugal, wato da Ingilishi 'The Struggle for Mozambique', An dauki littafin a matsayin mai tasiri bisa gwagwarmayar kasar.

  Yaya gwamnatin Mozambik ke tunawa da Eduardo Mondlane? An sauya sunan jami'ar da ke birnin Maputo fadar gwamnatin kasar zuwa sunan Eduardo Mondlane lokacin da kasar ta Mozambik ta samu 'yanci a shekarar 1975.

Wadanda suka taimaka da shawarwari wajen rubuta wannan tarihi sun hada da Farfesa Doulaye Konaté masanin tarihi da Dr Lily Mafela, gami da Farfesa Christopher Ogbogbo. Gidauniyar Gerda Henkel ce ta taimaka wajen kawo muku Tushen Afirka.