1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ecuador ta lallasa Qatar a wasan farko

November 20, 2022

A wannan Lahadin ce aka bude gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa a kasar Qatar, inda aka fara taka leda tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Qatar da kuma ta kasar Ecuador.

https://p.dw.com/p/4Jo2h
'Yan wasan kungiyar kwallon kafar ta Ecuador
Hoto: Ken Satomi/Yomiuri Shimbun/AP/picture alliance

An tashi wasan farko na wannan Lahadin ne Ecuador na da ci 2 yayin da mai masaukin baki ke nema. Dan wasa Enner Valencia na kungiyar kwallon kafar Ecuador ya samu nasarar saka kwallayen biyu a ragar mai masaukin baki wato kasar Katar. Ana dai ganin kasar Katar ta fadi kasa warwas a wasan bude gasar duk da watannin da ta dauka ta shirya masa. Wannan dai shi ne karon farko da wata kasa daga yankin Larabawa ta karbi bakuncin gasar wanda a wannan karo ke cike da cece-kuce.

Yarima Mohammaed bin Salman na Saudiya da Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas na daga cikin shugabanin da suka halarci bikin bude gasar da tawaga talatin da biyu daga kasashe talatin da biyu za su fafata.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan na musabaha da takwaransa na Masar Abdel Fattah al-Sisi
Hoto: Turkish Presidency/AP Photo/picture alliance

A wani labarin kuma, a karon farko shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi musabaha da takwaransa na Masar Abdel Fattah al-Sisi a kasar Katar. Wani hoto da fadar shugaban kasar Turkiyya ta wallafa, ya nuna yadda shugabannin suka yi musayar hannu tare da gaisawa a wajen bikin bude gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa a birnin Doha. Tun a shekarar 2013, shugabannin biyu suka fara takun saka sakamakon juyin mulkin da aka yi wa tsohon shugaban Masar Mohamed Morsi.