ECOWAS za ta gudanar da taro kan Burkina | Labarai | DW | 05.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ECOWAS za ta gudanar da taro kan Burkina

Za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Burkina Faso a baɗi,a ƙarshen wa'adin mulkin shekara guda na gwamnatin riƙon ƙwarya.

Shugaban ƙasar Ghana john Mahama Dramani kana shugaban Ƙungiyar gamayya tattalin arziki ta ƙasashen yankin yammacin Afirka wato ECOWAS.

Ya ce gwamnatin riƙon ƙwarya da za a girka a nan gaba a Burkina Faso za ta ɗauki tsawon wa'adin shekara guda,sannan ya ce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a cikin watan Nuwanba na shekarar baɗi kamar yadda aka tsara. A gobe Alhamis aka shirya Ƙungiyar ECOWAS za ta yi wani taro na musammun domin tattauna batun na Burkina Faso.