1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen mulkin soja

Binta Aliyu Zurmi
November 9, 2021

Kungiyar ECOWAS ta kakaba wa wasu sojojin mali jerin takunkumai.

https://p.dw.com/p/42m9S
ECOWAS Westafrikanische Staaten verhängen Sanktionen gegen Mali und Guinea
Hoto: Nipah Dennis/AFP

Sojojin da ke rike da madafun iko a kasar Mali sun bayana cewa suna da na sani a game da takunkumin da kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO ta kan wasu daga cikin sojojin da ke da hannu wajen kifar da gwamnatin farar hula har sau biyu a kasa da shekara guda.

ECOWAS ta dauki matakin kakaba takunkumin ne a karshen makon da ya gabata a birnin Accra na kasar Ghana, bayan da sojojin suka ce ba za su iya gudanar da zabe kamar yadda aka tsara yi cikin watan Fabrairun shekara mai zuwa ba.