Dusar kankara mai tsanani na sauka a Amirka | Labarai | DW | 24.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dusar kankara mai tsanani na sauka a Amirka

Ya zuwa wannan Lahadin a kalla mutane 19 ne suka rasu sakamakon zubar dusar kankara mai tsanani a wasu yankunan kasar Amirka.

Dusar kankara da ta fara zuba da yammacin Asabar a yankin Arewa maso Gabshin Amirkata yi sanadiyar rasuwar mutane 19 inda mafi yawansu sun rasu ne ta hanyar hadarin motoci tare kuma da haddasa ambaliyar ruwa mai tsananin gaske. Hukumomin dai sun samu kidaya mutane 13 da suka rasu sakamakon hadarin motoci a yankin Ohio, da Arkansas sannan wani mutun ya rasu a Maryland yayin da wasu uku suka rasu a birnin New York inda aka samu tudun dussar kankarar fiye da cm 60 da ta zuba a kasa a halin yanzu.

Daga nashi bangare gwamnan jihar New York Andrew Cuomo da ya ayyana dokar ta baci, ya bada izinin rufe dukannin wata gada da hanyoyin karkashin kasa da ke zuwa birnin na New York. Sannan kuma an soke duk wani harkokin suhuri a jihohin New York da New Jersey, inda a bangaran jiragen sama aka soke tashin jirage a kalla 5,100 a jranar Asabar, sannan a wannan Lahadi kuma aka soke a kalla tashin jirage 3,300.