Duniya ta yi wa Nelson Mandela fatan alheri | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 19.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Duniya ta yi wa Nelson Mandela fatan alheri

A ranar bikin cikarsa shekaru 95 da haihuwar, kasashe daban-daban na duniya sun gudanar da addu'o'i ga tsohon shugaban na Afirka ta Kudu.

Bari mu bude filin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta mayar da hankali kan bikin cikar Nelson Mandela shekaru 95 a duniya, inda ta fara da cewa.

"A lokacin da ya kai ziyara Afirka ta Kudu shugaban Amirka Barack Obama ya ce Mandela ya taka rawa bisa matsayin da Obaman yake yanzu. To sai dai Obama ne kadai ke sha'awara halayyar Mandela ba, ga daukacin 'yan Afirka ta Kudu tsohon dan gwagwarmayar kwatar 'yancin bakar fata na zama uba, wanda albarkacinsa kasar ta kawo karshen mulkin danniya da na wariyar launin fata. A ranar bikin cikarsa shekaru 95 da haihuwa 'yan kasar sun ci gaba da yi masa addu'ar samun lafiya bayan ya kwashe makonni shida yana cikin wani hali na rai kwakwai mutu kwakwai a wani asibitin birnin Pretoria."

Sadaukar da mintoci 67 na lokaci don gudanar da ayyuka na gari don girmama Mandela, inji jaridar Berliner Zeitung tana mai cewa 'yan Afirka ta Kudu sun gudanar da ayyuka na gari maras misaltuwa a ranar bikin zagayowar gwarzon kasar shekaru 95 da haihuwa. 'Yan kasar dai sun shirya wa wannan rana mai muhimmanci wadda tun a shekarar 2010 Majalisar Dinkin Duniya ta ayyanata a matsayin ranar Mandela don girmamawa ga irin sadaukar da ransa da yayi wajen yi wa jama'a aiki. Miliyoyin 'yan Afirka ta Kudu sun amsa kiran da hukumomi suka yi na sadaukar da mintoci 67 na lokacinsu don gudanar da aikin gaya da taimaka wa jama'a. Jaridar ta ci gaba da cewa wannan wani gagarumin aiki ne na jama'a da duniya ke alfahari da shi."

Tababa ga zaman lafiyar Mali

Sanagé Nana Coulibaly ist stolz auf ihre Wählerkarte *** Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 16. Juli 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Bamako, Mali

Shirye-shiryen zabe a Mali, Nana Coulibaly rike da katin zabe

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta buga labari ne game da kasar Mali tana mai gargadi da kar a yi riga Mallam masallaci. Ta ce zabukan gama gari da za a yi a kasar a ranar 28 ga watan Yuli za su nuna ko mulkin demokradiyya zai dawo kasar. Jaridar ta rawaito kalaman da shugaban rikon kwaryar Mali Dioncounda Traore ya yi a ranar Lahadi lokacin bikin kasar Faransa a birnin Paris wanda sojojin Mali suka shiga cikin faretin sojoji rike da tutar kasarsu. Shi dai Traore ya bayyana matakin sojin da Faransa ta dauka a Mali da cewa nasara ce ga nahiyar Afirka, nasara ce kuma a kan ta'addanci. Sai dai ba tun yau ba ake jin irin wadannan kalamai na samun nasara musamman tun bayan da sojojin Faransa suka fatattaki 'yan tawayen Islama daga arewacin Mali. Abin jira a gani shi ne ko zaben da za a yi a kasar a karshen wannan wata zai kawo sauyi mai ma'ana. Da yawa daga cikin masharhanta dai na fargabar cewa zaben ka iya zama mafarin sabon rikici kasancewa har yanzu ba a gama magance radadin rikicin kasar ba.

Rikicin gabacin Kongo

Mummunan bata kashi a gabacin Kongo, har wayau dai inji jaridar ta Süddeutsche Zeitung, sannan sai ta kara da cewa akalla mutane 120 aka halaka a wani gumurzu da aka yi tsakanin sojoji da 'yan tawaye a kusa da birnin Goma, amma dakarun Majalisar Dinkin Duniya ba su tsoma baki ba. Jaridar ta ce wannan fada na zama wani zakaran gwajin dafi ga sabbin dakarun Majalisar Dinkin Duniya tun ba a kammala tura su wannan yanki ba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe