Duniya ta manta da talaucin Nijar da Chadi | Labarai | DW | 06.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Duniya ta manta da talaucin Nijar da Chadi

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa abin kunya ne yadda aka yi wasti da tallafawa kasashe mafiya talauci a duniya, duk da alkawuran da aka yi na basu tallafi.

A cewar majalisar misali kasar Chadi a tallafin dala miliyan 527 da aka roki duniya su bata, kashi 17 cikin dari kawai aka samu. Haka ita ma Jamhuriyar Nijar dala 375 aka bukaci a taimakamata, amma kashi 25 cikin dari kacal ya samu. Jami'in kula da tallafi na MDD John Ging ya ce abun kunya ne yadda duniya ta manta da wadannan kasashen duk da cewa kasashen biyu sune mafiya talauci a duniya, a dai-dai lokacin da suke fama da 'yan gudun hijira daga kasashe makobta, wadanda suke fama da karancin hanyar samun abinci. Inda ya ce amma duniya ta mai da hankali ne kawai don agazawa kasashen da suka yi suna kamarsu Siriya da Sudan.