1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya ta fara gano yawan albarkatun noman da ke Afirka

April 26, 2013

Masu zuba jarin ƙasa da ƙasa sun gano cewa akwai albarkatun noma a Afirka, ta yaya za'a iya bunƙasa wannan fanni, ya dace da zamani ta yadda mutanen nahiyar zasu ƙaru da shi ba tare da an yi wani lahani ga muhalli ba?

https://p.dw.com/p/18O12
Senegalese members of a women farmers' group who received a loan from FEPRODES microfinance agency
Hoto: picture alliance/Godong

Ga girbin yawan amfanin gonan da bai taka kara ya karya ba ga kuma yawan filayen noman da ba'a amfani da su, Afirka yanki ne da ke da damar samun albarkatun noma masu yawa, kuma ko masu zuba jari sun gano wannan yawan albarkatun. To sai dai ta yaya za'a iya bunƙasa wannan fanni, ya  dace da zamani ta yadda mutanen nahiyar zasu ƙaru da shi ba tare da an yi wani lahani ga muhalli ba? Tambayar ke nan da masana a taron Afrikan Business Week da ke gudana a birnin Frankfurt na nan Jamus ke tattaunawa

Duk wanda ya zuba jari a fanin noman Afirka, kamata yayi ya tallafawa manoman ƙasashen domin inganta girbi da yawan amfanin gona shawara ke nan daga Mpoko Bokanga daga ƙungiyar bunkasa masana'antu na Majalisar Ɗinkin Duniya wato (UNIDO), duk wanda yayi wannan yadda ya kamata, zai rage yawan ƙauracewa filayen da ake yi yanzu.

Sabbin fasahohi za su hana matasa barin ƙauyuka

 "Za'a iya kawo sabbin fasahohi, naurorin yin noman zamani, waɗanda zasu ja hankalin matasa su so yin noma a gonakin, su kuma zo a dama da su wajen amfani da waɗannan naurori haka nan kuma zai bunƙasa yawan amfanin gonan da za'a samu saboda haka kowane ɓangare zai amfana"

Titel: Mpoko Bokanga Schlagworte: Mpoko Bokanga, UNIDO, Afrika, Landwirtschaft Wer hat das Bild gemacht?: Thomas Mösch Wann wurde das Bild gemacht?: 24.4.2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Frankfurt/Main Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Mpoko Bokanga, Chief of Agri-Business Development Unit, UNIDO. Bildrechte: Der Fotograf / die Fotografin ist (freie) Mitarbeiter(in) der DW, so dass alle Rechte bereits geklärt sind.
Mpoko BokangaHoto: DW

Samar da sabbin fasahohi kaɗai ba zai samar da sakamakon da ake so ba a cewar Bokanga. Saboda haka ne ita UNIDO ta ke la'akari da duk matakan noman baki ɗaya, daga huɗan filayen, irin shuka, da kuma shiryawa da sayar da albarkatun noman da aka samu

"Ya kamata mu duba mu ga wuraren da ke bukatar gyara, a yi gyaran, idan aka tallafa a mataki guda ba tare da la'akari da sauran matakan ba, jarin da ka zuba ba zai samar maka da irin riban da za ka samu idan da ka tallafa a dukkan matakan ba.

Buɗe hanyoyin cinikin amfanin gonan da aka samu

Wani wanda ya ɗauki wannan shawarar na tallafawa a dukkan matakan shine wani ɗan kasuwan Jamus Carl Heinrich Bruhn shugaban wani kamfani mai suna Amatheon. Amatheon tana so ta girka wani kamfanin noman da zai kawo riba sosai a Afirka ta yadda zata riɓanya jarin da ta zuba. A shirinsa na farko, Bruhn na da Hektar dubu 30 a Zambia wanda ya yi haya na tsawon shekaru 99. sun kuma sami filayen ta sahihiyar hanya dan saboda kada su faɗa cikin waɗanda ake zargi da satan filaye.

Titel: Carl Heinrich Bruhn Schlagworte: Carl Heinrich Bruhn, Amatheon, Sambia Wer hat das Bild gemacht?: Thomas Mösch Wann wurde das Bild gemacht?: 24.4.2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Frankfurt/Main Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Carl Heinrich Bruhn, CEO Amatheon Agri Holding NV, Betreiber eines landwirtschaftlichen Investitionsprojekts in Sambia. Bei der Africa Business Week 2013. Bildrechte: Der Fotograf / die Fotografin ist (freie) Mitarbeiter(in) der DW, so dass alle Rechte bereits geklärt sind.
Carl Heinrich BruhnHoto: DW

Kamfaninsa da wasu manoma sun fitar da wani tsari wanda zai amfani kowani ɓangare a cewar Bruhn. Manoman wannann yankin basu taɓa samun takin gargajiya ba bare ma iri da ma magungunan kare shuke-shuke ba

"Ta haka zamu samar da babban gona guda a tsakiya, inda zamu riƙa tura duk waɗannan abubuwan, da waɗannan kayayyaki, sai su ƙananan manoma su fara nasu gonakin, sai a mataki na biyu, da basu da kasuwannin saida kayayyakin da suka noma da kansu, saboda haka zamu sake samar musu da wannan dama, inda mu da kanmu zamu sayi waɗannan abubuwa da suka girba, sai mu yi amfani da motocinmu mu fitar da waɗannan kayayyaki zuwa babban birnin ƙasar inda za'a saida su.

Filayen noman na buƙatar tattali

Ƙungiyar kare muhalli ta duniya WWF tana shakkun wannan sha'awan da kamfanoni ke yi na samu filaye a Afirka. A haƙiƙa ita kanta tana sane da mahimmanci ƙara yawan abinci a cewar Birgt Wilhelm, wadda ke kula da sashin tabbatar da noma mai ɗorewa, na ƙungiyar ta WWF ta Jamus.

Haka nan kuma tana la'akari da cewa kashi 60 bisa 100 na filayen da ba'a yi amfani da su ba a duk faɗin duniya a Afirka su ke amma duk da haka, Birgit Wilhelm ta damu a kan cewa, filayen noman Afirka basu da ingancin sauran filayen da aka sani a duniya, kuma suna fama da rashin mahimman sinadaran da ake buƙata, ko su ma masu zuba jarin na sane da wannan.

Titel: Birgit Wilhelm Schlagworte: Birgit Wilhelm, WWF, nachhaltige Landwirtschaft Wer hat das Bild gemacht?: Thomas Mösch Wann wurde das Bild gemacht?: 24.4.2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Frankfurt/Main Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Birgit Wilhelm, Expertin für nachhaltige Landwirtschaft und Ressourcenschutz beim WWF Deutschland. Bildrechte: Der Fotograf / die Fotografin ist (freie) Mitarbeiter(in) der DW, so dass alle Rechte bereits geklärt sind.
Birgit WilhelmHoto: DW

"A kan ce filayen noman ba su da nagarta, ƙasar na buƙatar sinadaran da zasu inganta shi, shi ya sa ya kamata a sami takin gargajiya, ba tare da yin la'akari da tsari ko kuma yanayin muhallin da suke ba, abun na tattare da sarƙaƙiya, kuma yana nufin zuba jari a binciken kimiyya, wannan na nufin zuba jari na wani tsawon lokaci, idan har mutun zai zuba jari a fili kamata yayi ya kasance na wani tsawon lokaci aƙalla shekaru goma.

Mafi mahimmanci tana ganin cewa idan za'a zuba jari kan tsirai na samun makamashi, kada a yi shi cikin gaggawa domin hakan na da hatsari ga filayen.

Mawallafa: Thomas Mösch/Pinaɗo Abdu Waba
Edita:          Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani