Duniya ta ce sulhu ne mafitar rikicin Guinea | Labarai | DW | 03.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Duniya ta ce sulhu ne mafitar rikicin Guinea

'Yan adawar Guinea na son ganin an gudanar da zabukan kananan hukumomi kafin zaben shugaban kasa da za a yi a watan Oktoba, abin da shugaban ya ki bawa kulawa.

Alpha Condé Präsident Guinea

Alpha Conde shugaban kasar Guinea

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a yammacin Afrika ya bukaci bangaren gwamnati da na 'yan adawa a kasar Guinea da su gaggauta komawa kan teburin tattaunawa dan ganin an samar da zabe mai cike da tsafta a kasar.

Mohamed Ibn Chambas ya bayyana haka ne a ranar Talata a birnin Conakry yayin tattaunawa da manema labarai a lokacin ziyarar da ya kai wannan kasa ta Guinea.

Manzon na Majalisar Dinkin Duniya a yayin wannan ziyara ya kuma gana da shugaba Alpha Conde da wasu manyan 'yan siyasa da jami'an hukumar zaben kasar.

Wannan ziyara dai na zuwa ne bayan makwanni da aka dauka ana gwabza fada tsakanin masu fafutuka da ke adawa da gwamnati da jami'an tsaro a wannan kasa da ke a yammacin Afrika inda mutane da dama suka rasu wasu suka sami raunuka.

'Yan adawar na son ganin an gudanar da zabukan kananan hukumomi kafin zaben shugaban kasa da za a yi a watan Oktoba, abin da shugaban ya ki bawa kulawa, su kuma 'yan adawar suke zargin shugaba Conde da yunkurin daukar matakai na kankame iko da kananan hukumomin da za su iya taimaka masa a murde zaben shugaban kasa.