Duniya ta amince da yarjejeniyar nukliyar Iran | Labarai | DW | 20.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Duniya ta amince da yarjejeniyar nukliyar Iran

Majalissar Dinkin Duniyar ta amince da shirin yarjejeniyar da aka cimma da kasar Iran kan makaman nukliya kafin janye takunkuman da ke a kanta

Majalissar Dinkin Duniya ta bada sanarwar yin na'am da yarjejeniyar nukliyar da manyan kasashen yammacin duniya suka cimma da kasar Iran a makon da ya gabata.Kuma tuni ta soma shirye-shiryen daukar matakkan janye takunkumin tattalin arzikin da ta sakawa kasar ta Iran.

Sai dai Majalissar ta gitta sharadin cewa sai in hukumomin kasar ta Iran sun bawa hukumar Kula da makamashin nuklia ta duniya wato AIEA damar gudanar da bincike a kan tashoshin nukiliyar kasar tasu domin tabbatar da kasar ba ta a kan shirinta na neman kera makamin nukliya ne, kadai za a iya janye illahirin takunkuman da aka sakawa kasar tun daga shekara ta 2006.

Yanzu dai shingen karshe da ya rage wa wannan yarjejeniya ta tsallake shi ne na majalissar dokokin kasar Amirka da akasarin mambobinta ke adawa da ita,wacce za ta gudanar da zamanta a cikin watanni biyu masu zuwa domin bayyana matsayinta a kai