Duniya na yaki da yi wa mata kaciya | Zamantakewa | DW | 06.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Duniya na yaki da yi wa mata kaciya

A duk ranar shida ga watan Febrairu na kowace shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yaki da yi wa mata kaciya. Sai dai har yanzu lamarin ya na faruwa a wasu yankuna na Afrika.

Protest gegen Weiblicher Genitalverstümmelung (picture alliance/Pacific Press/M. del Mazo)

Yaki da yi wa mata kaciya

A gundumar Gaya cikin jihar Dosso mai makwabtaka da Jamhuriyar Benin wata mata ta bayyana yadda har yanzu ake yi wa mata kaciya a cikin kauyensu da ke tsakanin iyakar Nijar da Benin duk da cewa akwai masu adawa da hakan. Sai dai sannun a hankali za'a iya cewa an samu koma baya sosai a kan wannan dadadiyar al'ada. Wasu mata da ke cikin wadanda aka yi wa kaciya, wanda tuni aka yi musu aure a halin yanzu, sun danganta lamarin da mafi muni a cikin harkokin rayuwarsu, domin a cewarsu ba su da wata sha'awa a tsakanin su da mazajensu.

Daga na shi bangare shugaban babban asibitin birnin Gaya Docta Inoussa Gwanda, ya bayyana cewa lokaci zuwa lokaci suna samun matan da wannan al'ada ta kaciya ta fada a kansu musamman ma wadanda ke fitowa daga kasashe makofta su na zuwa asibitin domin duba lafiyarsu.

Kenia Mann trägt T-Shirt gegen Weibliche Genitalverstümmelung - Female Genital Mutilation FGM (Reuters/S. Modola)

Shaidar tuni da yaki da yi wa mata kaciya

Hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu sun dade suna wayar da kai dan ganin an kawo karshen yi wa mata kaciya. A cewar Barista Adam Aji, alkalin da ke kare kananan yara a mashara'ata ta birnin Gaya akwai dokokin da aka tanada na hukunta duk wadanda kama da laifin yi wa mata kaciya.