1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

MDD: Ana samu barazanar karancin abinci

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
November 8, 2021

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin al'ummar da 'yunwa ke yi wa barazana a wannan shekara ya karu sosai, idan aka kwatanta da na shekarar da ta wuce. Kasar Afghanistan ta kasance a kan gaba.

https://p.dw.com/p/42i69
Welthunger-Index | Dürre und schwerer Hunger im Süden Madagaskars
Hoto: Tsiory Andriantsoarana/WFP/dpa/picture alliance

Cikin wata sanarwa da ta fitar a birnin Roma na Italiya, Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 45 ne ke fuskantar barazanar karancin cimaka a bana, kana galibin wadanda suka kara adadin alkaluman sun fito ne daga kasar Afghanistan.

Annobar corona ma dai na daga cikin wasu dalilai da suka kara ta'azzara barazanar da duniya ke fuskanta a wannan shekara, a cewar babban daraktan hukumar David Beasley a yayin da yake zantawa da manaima labarai.