Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Shirin na kunshe da labarai da rahotanni daga sassa dabam-dabam na duniya.
Shirye-shiryen Ji Ka Karu da Zabi Sonka da Ra'ayin Malamai za su biyo bayan labaran duniya.
A cikin shirin akwai labaran duniya da shirye-shirye dabam-dabam.
Jam'iyyar PDP ta adawa a Najeriya ta dau hanyar shawo kan matsalolin da suka hanata rawar gaban hantsi a siyasar kasar.
A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya jam'iyyar adawa ta PDP ta dauki hanyar dinke rikicin cikin gida da ya kunno mata, a Nijar sabin membobin hukumar koli mai kula da kafafen sadarwar kasar watau CSC sun sha rantsuwar kama aiki.
Akalla mutane tara ne suka mutu a wani turmutsitsin da ya barke a birnin Karachi da ke kudancin Pakistan,yayin da jama'a suka garzaya zuwa wata masana'anta da aka shirya rabon sadaka na azumin Ramadan
A cikin shirin za a ji martanin 'yan Nijar kan matakin gwamnatin Jamus ta na amincewa da aika karin sojoji domin bai wa sojojin kasar horo a fannin yaki da ta’addanci, a Amurka tsohon shugaban kasar Donald Trump na daf da zama tsohon shugaban Amurka na farko da doka za ta buga bisa aikata babban laifi.
A wannan makon mun tattauna ne kan irin abincin da ya dace mai Azumi ya yi amfani da su yayin da yake wannan muhimmin ibada. Kwararru sun yi karin haske har da irin abincin da za a kauce musu domin kare lafiya.
Yan takarar da suka yi nasara a zabukan da suka gabata a Najeriya na ci gaba da murnar samun galaba, amma wani hali wadanda suka sha kaye a zaben ke ciki?
Shirin ya duba shigowar zafi a kasashen Afrika da cututtuka da ya kamata a yi kokarin kaucewa kamuwa da su.
Shirin ya kunshi yaba wa rawar kafofin sada zumunta a arewacin Najeriya. Akwai taimako da kungiyoyi ke kara yi a kudancin Najeriya ga wadanda ke Azumi. A Ghana kamfanonin atamfa ne ke fuskantar bazanar rugujewa saboda karuwar shigar atamfofi daga ketare.
A cikin shirin za a ji cewa: Kotun kasa da kasa ta yi watsi da bukatar Iran ta cire kudadenta da Amurka ta rike, Kasashen EU sun cimma matsaya ta ninka yin anfani da makamashin da ake sabuntawa nan da zuwa shekarar 2030.
A Jamhuruyar Nijar a yayin da hankula suka fara karkata kan abinci nagari mai gina jiki da koshin lafiya, masana sun kirkiri bikin nuna al'adar girke-girken abincin gargajiya irin na Agadez
Makomar matasa 'yan Social Media da ke yada manufofin 'yan siyasa a kafofin sada zumunta
An zargi Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da neman yin katsalandan a shugabancin Kano
Sarki Charles na III na Birtaniya ya iso nan Tarayyar Jamus don fara ziyarar aiki ta tsawon kwanaki uku, inda zai gana da shugaban gwamnatin kasar Olaf Scholz da sauran kusoshin gwamnati.
Shirin na dauke da labaran duniya da rahotanni ciki har da darussan da 'yan siyasa da ba su sami damar yin nasara a zaben ba suka dauka a Najeriya.