Dubban ′yan sanda sun yi zanga-zanga a Tunisiya | Labarai | DW | 25.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dubban 'yan sanda sun yi zanga-zanga a Tunisiya

A kalla 'yan sanda 3,000 ne suka yi jerin gwano a wannan Litinin din a birnin Tunis na kasar Tunisiya ya zuwa fadar shugaban kasar ta Chartage domin neman karin albashi.

'Yan sandan na rera cewa albashinsu dai bai taka kara ya karya ba, sannan kuma sune ke sadaukar da rayukansu wajan kariyar kasa, don haka suna bukatar abun da suke gani halaliya ne a gare su. Jami'an tsaron kasar Tunisiya dai na taka rawar gani wajan yaki da 'yan kungiyar IS inda su ne kuma kan gaba wajan fuskantar hare-haren 'yan kungiyar, inda a bara ma aka kaiwa jami'an da ke tsaron shugaban kasar hari tare da hallaka da dama daga cikin su.