matakin 'yan gudun hijira na shiga Amirka
November 10, 2018Rahotanni daga kasar Mexiko na cewa ayyarin mutane kimanin dubu biyar 'yan gudun hijira masu burin shiga kasar Amirka ko ta halin kaka, sun dauki hanyarsu a wannan Asabar inda suke tafiya a kafa duk kuwa da tarin gajiya da ma rashin lafiya.
Tun dai a ranar Alhamis 'yan gudun hijiran sun nemi hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijira ta ba su taimakon motocin safa har 150 domin su kara gaba, sai dai ganin hakarsu ba ta cimma ruwa ba, ayyarin masu neman shiga kasar ta Amirka sun ci gaba da tafiya a kafa.
Tun dai daga ranar 13 ga watan Oktoba ne ayarin mutanen ya bar birnin San Pedro Sula na kasar Honduras a wani mataki na gujewa matsalar talauci da tashe-tashen hankulla da suka yi musu katutu da zimmar zuwa kasar Amirka. Sai dai shugaban kasar ta Amirka Donald Trump ya danganta wannan mataki a matsayin mamaya.