1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 43 sun hallaka a Kwango

Abdoulaye Mamane Amadou
April 27, 2020

A Jamhuriyar Dimukuradiyar Kwango an hakalla mutane 43 a sakamakon wani gumurzun soja da 'yan tawaye a yankunan Ituri da Kivu da ke arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/3bTwm
Ruanda-Rebellen von Sylvestre Mudacumura befehligt
Hoto: AFP/L. Healing

Shedun gani da ido sun shedawa kamfanin dinalnacin labaran Faransa AFP cewa wasu sojoji biyu sun rasa ransu a ayayin batakashir da aka shafe tsawon wunin jiya Lahadi ana yi tsakanin soja da mayakan na sa kai, ko da yake sojojin sun yi nasarar hallaka 'yan 12 daga cikinsu.

A Lardin arewacin Kivu mai makwaftaka da Beni, wasu mayakan da ake kyautata zaton membobin kungiyar ADF ne sun hallaka mutn shida, ciki har da wani shugaban al'umma, sai dai matsalar kashe-kashen ta fi muni ne a a kauyen Mahagi na Lardin Ituri, inda mayakan suka hallaka mutum 21 daukacinsu fararen hula a raranr Juma'ar da tagabata.