1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Donesk ta ce ta balle daga Ukraine

April 7, 2014

Kwana daya bayan fara zanga-zanga 'yan aware na gabashin Ukraine sun ayyana yankin Donesk a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

https://p.dw.com/p/1BdIa
Pro-russische Proteste in Donezk, Ukraine 06.04.2014
Hoto: picture-alliance/dpa

Masu zanga-zangar goyon bayan Rasha a Ukraine sun ayyana yakin Donetsk da ke gabacin kasar a matsayin kasa mai cin gashin kanta, kwana daya bayan kayar da baya da suka tayar da nufin neman ballewa daga kasarsu. Tun da farko dai sun yi wa wasu gine-ginen gwamnati ciki har da fadar gwamnan Dontsk kawanya kafin daga bisani su mamayeta.

Shugaban Ukraine wanda da farko ya kira taron gaggawa da manyan hafsoshin tsaro, ya zargi Rasha da marar hannu a wannan rikici domin a cewarsa rarraba kawunan 'yan kasar. Idan za a iya tunawa dai shugaba Vladimir Putin ya yi alkawarin daukan matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin 'yan Ukraine da ke da tushe da Rasha.

Kanfanin dillancin labaran Interfax na Rasha ya ruwaito cewa 'yan aware na Donesk na da niyar gudanar da zaben raba gardama kafin 11 ga watan mayu mai zuwa domin bai wa 'yan yankin damar bayyana inda suke so suka kasance.

Kasashen yammacin duniya sun yi barazanar sake kakaba wa Rasha sabbin takunkumai idan suka sameta da hannu a wannan sabon rikici na ukraine.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman