1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko Donald Trump zai iya rasa mulki ?

Gazali Abdou Tasawa AH
December 19, 2019

'Yan siyasa da masu sharhi kan harakokin yau da kullum a Afirka sun soma bayyana matsayinsu dangane da matakin majalisar wakilan Amirka na kada kuri'ar amincewa da tsige shugaba Donald Trump.

https://p.dw.com/p/3V6WG
USA Ankunft von US-Präsident Donald Trump in Battle Creek, Michigan
Hoto: Reuters/L. Millis


Da take tsokaci dangane da wannan mataki da majalisar wakilan Amirkar ta dauka da ke zama matakin farko da zai kai ga tsige shugaba Donald Trump daga kan mukaminsa, Malama Naja'atu Mohammed wata 'yan siyasa a Najeriya cewa ta yi wannan ya nuna irin ci gaban da tsarin dimukuraddiyyar Amirka yake da a kan na sauran kasashe musamman na Afirka. Ta ce: ''Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da majalisar wakilai ta Amirka ke kada kuri'ar amincewa da tsige wani shugaban kasar da ake zargi da aikata wani laifi.''  A baya ma shugaba Andrew Johnson shugaba na 17 na Amirka da kuma Bill Clinton shugaba na 42 na Amirka sun taba fuskantar wannan mataki. Kuma a cewar Dokta Nuhu Salifou Jangorzo malami a jami'ar birnin Maradi kana mai sharhi kan harakokin yau da kullum akwai babban darasi da ya kamata kasashen Afirka su dauka a cikin wannan mataki da majalisar wakilan na Amirka ta dauka kan Donald Trump.

Akwai wuya masu fafutukar tsige Donald Trump din daga mulki su yi nasara

USA Trump Amtsenthebung
Hoto: picture-alliance/AP Photo/House Televiwion

A baya dai shugabanni biyu na  Amirka Johson da Clinton sun yi nasarar ketara siradin yankan kauna tsigesu daga kan mukamin nasu bayan daga karshe majalisar dattawan kasar wacce ita ce ke da karfin ikon iya tsige shugaban kasar ta yi watsi da mataki. Kuma Malama Naja'atu gogaggiyar 'yar Siyasa a Najeriya ta ce ko a wannan karo da wuya hakar masu neman tsige shugaba Trump din ta iya cimma ruwa. Nashi bangare Shugaba Richard Nixon shugaba na 37 na kasar ta Amirka ya yi murabus ne daga kan mukamin nasa tun kafin majalisar wakilan kasar ta kai ga kada kuri'ar amincewa da tsigeshi a sakamakon badakalar Watergate. Yanzu dai jama'a sun zura ido su ga yadda za ta kaya a gaban majalisar dattawan kasar a game da wannan yunkuri na neman tsige shugaba Donald Trump dan shekaru 73 da ke zama shugaba na 45 na kasar ta Amirka.