Dokar takaita zirga-zirga a Nasarawa | Labarai | DW | 17.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar takaita zirga-zirga a Nasarawa

Rahotanni daga jihar Nasarawa da ke Tarayyar Najeriya sun nuna cewar an kafa dokar hana fita daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safiya.

Da yammacin Litinin din nan ne dai gwamnatin jihar ta sanar da dokar, bayan wani taron da majalisar tsaron jihar tayi, biyo bayan wani tashin hankali da ya auku a kauyen Alakyo, inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi da dama. Wakilinmu na jihar ta Nasarawa Abdullahi Maidawa Kurgwi, ya ruwaito cewa rikicin dai ya bazu zuwa garin Lafiya fadar gwamnatin jihar, da kuma kauyuka mafi kusa. Tun da fari dai an rufe makarantu da bankuna da kuma kasuwanni a garin na Lafiya. Wani mazaunin garin Lafiyan ya ce an soma kone konen gidaje tare da kashe wasu mutane 3, a garin. Yanzu haka dai an tura jami'an tsaro daga barikin sojoji da ke garin Keffi inda kowa ya shiga gida kuma babu kowa a kan titunan garin na Lafiya da kewaye sakamakon wannan doka ta hana fita.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane