Dokar ta baci a Mali da Tunisiya bayan ayyukan 'yan ta'adda
December 23, 2015Talla
A ranar Talata gwamnatin kasar Mali ta ayyana kafa dokar ta-baci yayin da kasar Tunisiya kuma ta tsawaita tata dokar ta-bacin da watanni biyu. Dokar ta-bacin a Mali za ta yi aiki tsawon kwanaki 10 ta kuma biyo bayan wani hari ne da aka kai kan otel din Radisson Blu da ke birnin Bamako, ranar 20 ga watan Nuwamba, inda aka halaka mutane 20 ciki har da baki 'yan kasashen waje.
Ita kuwa gwamnatin Tunisiya ta tsawaita dokar ta-baci da watanni biyu bayan wasu hare-haren ta'addanci guda uku da suka girgiza kasar. Akalla mutane 75 aka kashe a hare-haren ta'addancin na baya-bayan nan. Yanzu haka an kafa dokar takaita zirga-zirga a babban birnin kasar Tunis, yayin da kuma aka rufe kan iyakar kasar da kasar Libiya.