1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar soji na barazana ga demokradiyya a kasar Thailand

May 20, 2014

Al'ummar Thailand na fargabar watakila dokar sojin da aka sanya a kasar zai rikida zuwa juyin mulki wanda zai kasance babban barazana ga wanzuwar demokradiyya a kasar

https://p.dw.com/p/1C3Ln
Thailand Armee verhängt Kriegsrecht 20.05.2014
Hoto: Reuters

A yayin da kasar Thailand ke kammala wunin farko da dokar da ta baiwa sojoji wuka da nama su gudanar da harkokin kasa, jama'a na dasa ayar tambaya kan sahihancin wannan matakin, inda da yawa ke ganin cewa zuwan sojoji Bangkok tamkar juyin mulki wanda ka iya tasiri kan wadanda ke zama a birnin.

Dakarun sojin dai sun kare wannan matakin da suka dauka da cewa akwai bukatar su tabbatar da doka da oda, bayan da aka dade ana zanga-zangar siyasa, inda a wasu lokuta ma ake amfani da makamai. A harin da aka kai baya-bayan nan an yi amfani da gurneti kan masu zanga-zanga a birnin Bangkok inda har mutane uku suka mutu, wasu 20 kuma suka ji ciwo

Jagoran masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar dai ya yi ikirarin cewa wannan ne mako na karshe a gwagwarmayar da suka yi na kifar da gwamnati, shi ya sa dakarun sojin suka dauki wannan matakin dan ganin cewa an kare fararen hula daga shiga cikin wani mummunar hali. Ga dai abin da wasu yan kasar suka fada da aka tambaye su ra'ayoyinsu dangane da dokar sojin da kan kasar yanzu

Thailand Armee verhängt Kriegsrecht 20.05.2014
Sojoji sun mamaye birnin BangkokHoto: Reuters

Ra'ayoyin 'yan kasa dangane da dokar soji

Wannan matar cewa ta ke yi, a gaskiya ina farin cikin cewa wani na kokarin tabbatar da cewa an sami zamna lafiya da kwanciyar hankali a kasa

Shi kuma wannan mutumi, ya ce a gani na ya kamata a ce tun tun tuni ne dakarun sojin suka dauki irin wannan mataki

A halin da ake ciki kuma kungiyar masu jajayen kaya wadanda ke goyon bayan gwamnati na cigaba da taruwa a wajen birnin Bangkok kuma dakarun sojin kasar sun ce daya daga cikin dalilan da ya sanya su shiga tsakanin rikicin ke nan dama, domin su kare bangarorin biyu daga tabka artabu.

Madafun iko sun zame daga hannun gwamnatin riko

Da wannan yanayi da aka shiga yanzu, gwamnatin rikon kwaryar Thailand za ta cigaba da rike iko, duk da cewa ba ta yi kama da gwamnatin da ke da sauran iko a hannunta ba domin ko a ranar talata Firaministan riko Miwattumrong Boonsongpaisan sai da ya jira na tsawon sao'i 12 kafin ya mayar da martani ga sanarwar sojojin, kuma wata majiya ta ce firaministan na boye a wani wuri da ba a tantance ba, inda ya gana da majalisar ministocinsa, ya kuma sami labarin cewa ko su sojojin ba su yi shawara da su ba kafin suka ayyana dokar soji a kasar Jatuporn Prompan shi ne shugaban kungiyar masu jajayen riguna

"Idan Janar din ya bukaci aiwatar da abin da ya fi, idan ya bukaci da a gudanar da juyin mulki, zai zamana cewa masu jajayen kayan ba su da wani zabin da ya fi da ya wuce su cigaba da gwagwarmaya har sai sun tabbatar da wanzuwar demokradiyya"

Timeline Thailand
Masu jajayen kaya sun ce za su kare demokradiyyaHoto: picture-alliance/dpa

Shugaban rundunar sojin kasar dai bai fadi sadda dokar za ta daina aiki ba, abin da ya ce shi ne, tsawon dokar ya daganci sadda aka kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar. A yayin da kasashen duniya ke ta bayyana ra'ayoyinsu dangane da wannan dokar sojin da ta fara aiki a kasar ta Thailand, tsawon yau an wuni ne dakarun suna dakatar da labarai a tashoshin kasar domin bayar da sanarwar sabbin sharuddan da za su yi amfani da shi a karkashin wannan doka dama dai yadda za su fadada ikonsu wajen gudanar da hidimomin kasa.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu