David Mark dan siyasa ne a Najeriya wanda ya taba rike mukamin shugaban majalisar dattawan kasar na tsawon lokaci.
Mark ya kasance guda daga cikin 'yan majalisar dattawan kasar da suka jima a zauren majalisar daga lokacin da mulki ya koma hannun farar hula a shekarar 1999. Gabannin shigarsa siyasa dai ya yi aikin soja inda ya kai mukamin Birgediya Janar kafin ya yi ritaya.