David Cameron ya nemi Scotland ta zauna cikin Birtaniyya
September 10, 2014Mako guda gabanin kuri'ar raba gardama game da 'yancin kan yankin Scotland, Firaministan Birtaniyya David Cameron ya yi kira da ci gaba da zaman Daular Birtaniyya a matsayin kasa daya al'umma daya. Ya fadi haka ne a birnin Erdinburgh inda ya kara da cewa Birtaniyya wani iyali ne na kasashe wadda kuma tun shekaru 300 da suka wuce yankin Scotland ke cikinta don radin kai. Cameron da mataimakinsa kuma dan jam'iyyar Liberal Democrat Nick Clegg da jagoran 'yan adawa na Labour Ed Miliband suna yankin a kokarin shawo kan masu kada kuri'a na Scotland su amince da zama cikin kasar Birtaniyya. A ranar 18 ga watan nan na Satumba 'yan Scotland za su yi zabe raba gardama game a ballewar yankinsu daga Birtaniyya. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa ana kafada da kafada tsakanin masu adawa da masu goyon bayan samun 'yancin kan.