Daukar tsauraran matakan tsaro a Sahel | Labarai | DW | 14.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daukar tsauraran matakan tsaro a Sahel

Ministocin yankin Sahel da Magreb sun hallara a birnin Rabat din kasar Moroko, domin tattauna hanyoyin bunkasa tsaro da kare kan iyakokin kasashen daga 'yan tawaye

Ministocin harkokin waje na kasashen da ke yankin Sahel da Magreb, suna taro a birnin Rabat din kasar Moroko domin tattauna matakan inganta tsaro kan iyakokin su tare da kalubalantar masu tsattsauran ra'ayi da ke barazana a yankin. Anasaran halartar manyan jami'an Amurka da Birtaniya da Faransa. Taron dai a cewar ministan sadarwan Moroko Mustafa Khalfi, na da nufin samar da hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin, tare da sanya fifiko kan kasashen Mali da Libiya. Har yanzu dai kasar Mali na fuskantar hare hare na mayakan tawaye, watanni 10 bayan da dakarun Faransa suka kai somame a kan kungiyoyin 'yan tawaye da ake alakantawa da ta Al-Qaeda, wadanda suka samu gindin zama a yankin arewacin kasar, inda aka yi wa wasu 'yan jaridar Faransa kisan gilla a farkon watan Nuwamba. Kwararru kan tsaro dai sun yi gargadin cewar, a yanzu haka irin wadannan kungiyoyin tarzoma na samun gindin zama a cikin sahara da ke kudancin Libiya.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Pinado Abdu-Waba