Daukaka shari′ar Oscar Pistorius | Labarai | DW | 09.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daukaka shari'ar Oscar Pistorius

An dai yanke wa Oscar zaman gidan wakafi na tsawon shekaru biyar inda za a sake shi ya koma daurin talala bayan watanni goma. Hukuncin da masu fafutuka a kasar Afrika ta Kudu ke ganin ya yi sassauci.

A gobe Laraba alkali mai sauraren kara zai mai da bayani kan cece-kucen da ake yi ko za a sake bari masu gabatar da kara su daukaka kara da su ke son yi, kan hukuncin da aka yanke wa Oscar Pistorius, dan wasan nakasassun nan na Afrika ta Kudu da aka yanke wa hukunci bayan kisan budurwarsa.

A watan Oktoba ne dai mai shari'a Thokozile Masipa ta ca ji Pistorius da laifin kisan budurwarsa, ba da ganganci ba, inda ta yanke masa zaman gidan wakafi na tsawon shekaru biyar da za a sake shi ya koma ana masa daurin talala a gida bayan watanni goma.

A cewar mai gabatar da kara Gerrie Nel idan har aka bada damar daukaka kara to babu abinda zai hana su nemi a yi masa hukunci mai tsaurin da ma ya wuce wanda alkali Thokozile Masipa ta yi masa .