Daukaka karar Sadam | Labarai | DW | 06.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daukaka karar Sadam

Anasaran cewa kotun daukaka karar hukuncin kisa ta hanyan rataya da aka yankewa Sadam Hussein ,zai gabatar da hukunci a tsakiyan watan Janairu shekara mai kamawa.Ayau nedai Alkalai suka fara gudanar da shirye shiryen daukakan karan tsohon shugaban na Iraki ,adai lokacin da aka dage dokar hana fita da aka kafa tun ranar asabar a wannan kasa saboda gudun barkewar rikici.A hannu guda kuma prime minista Nuri al-Maliki yayi kira ga jamian tsaron kasar dasu dauki tsauraran matakan aiwatar da dokar yaki da ayyukan tarzoma,domin kare barkewan rigingimu na bangarorin adawa.Kazalika ya kumayi gargadi wa kafofin yada labarai,adangane da yayata rahotanni da zasu iya tada zaune tsaye.Tuni dai mazarta suka bayyana hukuncin na Sadan da kasancewa wata kafar ruruta rikici a Irakin,da a halin yanzu ke fama da rigingimu.Ayayinda yan darikar Shia ke cigaba da bukukuwan murna, a daya hannu larabawa yan Sunni ,sunyi adawa da wannan hukunci akan hambararren shugaban gwamnatin Irakin.