Dattawan Najeriya sun yi ma kundin tsarin mulki gyaran fuska | Siyasa | DW | 21.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dattawan Najeriya sun yi ma kundin tsarin mulki gyaran fuska

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da sauye-sauyen da aka gudanar a tsarin mulki ciki har da batun bayar da cikakken 'yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi.

Daukacin ‘yan majalisar dattawan Najeriyar ne suka amince da wadannan sauye-sauye har 71 da aka dade ana jan kafa a kansu. Sai ma da ta kai ga kafa kwamitoci na musamman don su daidaita sabanin da ke a tsakanin abubuwan da majalisar wakilan kasar ta jefa kuri'a tare da amincewa da su.

Sassan da suka fi dauka hankali dai sun hada da batun cire kariyar ga shugaban Najeriya da mataimakinsa da ma gwamnonin kasar. Sai kuma dokar nan da ta bai wa kananan hukumomin Najeriya cikakken ‘yancin cin gashin kansu.

Nigeria Tag der Demokratie

Shugaban kasa da mataimakinsa ma dotar da shafesu

Sanata Hadi Sirika ya bayyana muhimmancin wadannan sauye-sauye ga kokarin kyautata mulkin dimukurdiyya. Ya ce idan aka sakar wa kananan hukumomi mara, ‘' za'a fara ganin cewa kudadden da ake tura masu suna amfani dda shi omin al'umma. Sannan maganar janye kariya ga shugaban kasa da gwamna wannan babban al'amari ne da zai canza yadda mutane suke yi wa doka karar tsaye''.

Baki ya zo daya a tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai a aikin gyara ga tsarin mulkin Najeriyar. Sai dai kuma Sanata Ali Ndume ya ce ‘' sai an zaga da shi zuwa jihohi kuma an samu kasha biyu bisa uku na 'yan majalisun ko kuma akalla jihohi 24 sun amince da shi tukunan, a yi gyara kafin shugaban kasa ya sa hannu,sannan ya zama doka ba''.

Kwarrau na ganin cewa da sauran jan aiki a gaba saboda sanin yadda ‘yan majilsun dokoki na jihohi suka zama tamkar ‘yan amshin shata ga gwamnoninsu, wadanda a fili suke adawa da baiwa kanana hukumomin cikakken ‘yan kansu, saboda yadda suka maidasu tamkar saniyar tatsa ga kudadden da ake basu daga asusun tarayya.

Sauti da bidiyo akan labarin