Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Yan takarar da suka yi nasara a zabukan da suka gabata a Najeriya na ci gaba da murnar samun galaba, amma wani hali wadanda suka sha kaye a zaben ke ciki?
Yan takara da suka sha kaye a zaben Najeriya na 2023, na shirin shigar da kara a gaban kotu domin kalubalantar sakamakon da Hukumar INEC ta fitar.
Sakamakon zaben da Hukumar INEC ke fitarwa ya janyo tayar da jijiyoyin wuya daga jam'iyyun hamayya da ke kira na a dakatar da aikin.
A ci gaba da shirye-shiryen kamun iko, sabon shugaban Najeriya da ke shirin hawa gado ya yi watsi da batun gwamnatin hadin kai na kasa da masu adawa ke neman gani cikin kasar bayan zabe mai zafi.
Rahotanni daga Najeriya na cewar wasu jihohi 6 daga cikin jihohin da suka shigar da kara gaban kotun koli domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da ya baiwa Bola Ahmed Tinubu nasara sun janye wannan matakin.