Darajar kudin Afirka ta Kudu ya tashi | Labarai | DW | 27.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Darajar kudin Afirka ta Kudu ya tashi

Kudin Afirka ta Kudu ya samu tagomashi a kasuwar hada-hada bayan garambawul da Shugaba Cyril Ramaphosa ya yi ga gwamnatin kasar.

Darajar kudin Afirka ta Kudu ta haura da maki 0.8 cikin 100 bayan garambawul na majalisar ministoci da Shugaba Cyril Ramaphosa ya yi ga gwamnatin kasar. Tuni aka yi waje da magoya bayan tsohon Shugaba Jacob Zuma daga cikin ministocin sannan aka sake dawo da mutanen da Zuma ya sallama daga bakin aiki.

Karkashin sabon zubin Nhlanla Nene ya zama ministan kudi, kana Pravin Gordhan da ake girmamawa a kasashen duniya zai jagoranci ma'aikatar kula da kaddarorin gwamnati. Sannan Shugaba Ramaphosa ya nada David Mabuza firimiya na Lardin Mpumalanga a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa. Sai dai akwai zargin sabon mataimakin shugaban kasar na Afirka ta Kudu yana da hannu a tashe-tashen hankula na siyasa da ake fuskanta a kasar.

Yayin da aka sallami akasarin magoya bayan tsohon Shugaba Jacob Zuma daga cikin gwamnati, a wani bangare tsohuwar matarsa Nkosazana Dlamini-Zuma ta zama minista a fadar shugaban kasa, kuma ta nemi shugaban jam'iyyar ANC tare da shugaban kasar Cyril Ramaphosa.