Dangantakar talauci da kiwon lafiya | Siyasa | DW | 07.04.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dangantakar talauci da kiwon lafiya

A sakamakon matsaloli na talauci har yau ana fama da tafiyar hawainiya wajen samar da wata nagartacciyar hanyar kiwon lafiya ga kowa-da-kowa a kasashe masu tasowa

A kasashe masu ci gaban masana’antu, ko da yake an dauki, mutuncin dan-Adam da muhimmanci, musamman idan magana ta shafi makomar rayuwa, kamar yadda aka gani baya-bayan nan dangane da gwagwarmayar da iyayen Terri Shiavo suka rika yi domin ceto ‚yar tasu dake kwance rai hannun Allah a ‚yan makonnin da suka wuce. Amma fa abin mamaki tun da ake ba a taba samun wata gwamnati da ta kira wani zama na gangami ko gabatar da wani kuduri dangane da barazanar da mata da yara ke fuskanta wajen haifuwa ba. Babu wata dokar dake kare makomar rayuwar uwayen yara da ‚ya’yansu a kasashe matalauta dake tasowa. Akwai cikakkiyar kafa ta dakatar da kaddarar barin haifuwa da kan rutsa da jarirai sama da miliyan uku a shekara, da kuma wasu yara miliyan 11 da kan yi asarar rayukansu kafin su samu shekaru biyar na haifuwa. Akwai matakai iri dabam-dabam da za a iya dauka domin tinkarar wannan matsala, kama daga wayar da kan jama’a zuwa ga manufofi na tsaftar muhalli da ruwan sha da kuma wasu ‚yan magunguna na kiwon lafiyar yara ko kuma irin shirye-shiryen nan na rage yawan haifuwa, wanda zai iya taimakawa wajen ceton makomar rayukan kashi daya bisa uku na matan da kan yi asarar rayukansu a shekara. Muddin aka ci gaba da yi wa matsalar mace-macen yara da uwayensu mata rikon sakainar kashi, musamman ma a nahiyar Afurka inda mace daya kan mutu a tsakanin mata 16 a lokacin haifuwa, to kuwa da wuya a cimma burin da taron duniya akan bunkasar yawan jama'a da aka gudanar a alkahira a shekara ta 1994 ya sa gaba. Kungiyar likitoci ta duniya ta sha nanata kuka a game da rashin magunguna wajen jiyyar yaran da suka kamu da kwayoyin cutar Aids a kasashe masu tasowa. Lafiya dai, kamar yadda Hausawa su kan ce, ita ce uwar jiki, wannan kuma shi ne ainifin dalilin da ya sanya kasashe masu ci gaban masana’antu ke kashe makudan kudi a manufofinsu na kiwon lafiya. Kuma ko da yake wannan hakkin wadannan kasashe ne, amma a daya bangaren abin takaici ne ganin yadda ake sako-sako da makomar lafiyar yara da uwayensu a kasashe masu tasowa, lamarin dake yin nuni da gaskiyar cewar ba a mutunta rayuwar al’umar wadannan kasashe. Tilas ne a samu canji ga salon tunanin wadanda alhakin al’amura ya rataya a wuyansu, musamman idan ana batu a game da girmama hakkin dan-Adam, saboda, kamar yadda muka fada tun farko, kiwon lafiya wani bangare ne na hakkin dan-Adam a wannan duniya ta mu.