Dangantakar Amirka da Saudi Arebiya | Labarai | DW | 28.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dangantakar Amirka da Saudi Arebiya

Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya isa kasar Saudi Arebiya a wani mataki na inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Wannan dai shine karo na farko da Shugaba Barack Obama na Amirkan ya kai ziyara kasar ta Saudiya tun daga shekara ta 2009. Bayan da ya isa Obama ya fara ganawa da Sarki Abdullah na Saudiyan ganawar da wani babban jami'in fadar gwamnatin Amirkan ya ce za ta mayar da hankali ne kan al'amuran tsaro a kasashen yankin tekun Fasha da Siriya da Iran da kuma kokarin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Masar. Obama dai na samun rakiyar Sakataren harkokin kasashen waje na Amirkan John Kerry da kuma mai bashi shawara a kan al'amuran tsaro Susan Rice.

Da yake ganawa da Obama a gidan gonarsa na Rawdat Khuraim dake arewa maso gabashin babban birnin kasar Riyadh, Sarki Abdullah da ya samu rakiyar 'yan masauratar ta Saudiya ya bukaci Amirka da ta canza salon matakan da take dauka a kan rikicin Siriya musamman abun da ya kira da tafiyar hawainiya da Washington din ke yi wajen baiwa 'yan tawayen Siriyan makamai masu linzami da za su iya kakkabo jiragen sama. Saudiya dai na goyon bayan 'yan tawayen Siriya a kokarin da suke na ganin bayan gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad na Siriyan. Haka kuma Sarki Abdullah zai tattauna batun yarjejeniyar da ake shirin cimma a tsakanin Iran da kasashen yamma kan batun makamashin nukiliyar Iran din wanda shima yake ciwa Saudiyan tuwo a kwarya.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar