Dangantaka tsakanin Kamaru da Afirka ta Tsakiya | Zamantakewa | DW | 11.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Dangantaka tsakanin Kamaru da Afirka ta Tsakiya

Rikicin tawaye da ake fama da shi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya fara yin mummunan tasiri a ma'amalarta da makobciyarta Jamhuriyar Kamaru a fannoni daban-daban.

Katon dubu uku da ke makare da magunguna ne suka shafe kwanaki a kan iyakar Kamaru da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, sakamakon yajin aiki da direbobin da alhakin jigilarsu i zuwa Bangui ya rataya a wuyansu suka yi. Sun zargin 'yan tawayen Seleka da gallaza musu, alhali za a yi amfani da wadannan magungunan ne domin ceto kananan yaran Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ke fama da karancin abinci mai gina jiki . Ko da su ma takwarorinsu direbobin tireloli, sai da suka shafe kwanaki ba tare da debo kayayyakin bukatun yau da kullum daga tashar jirgin ruwa na Doualan Kamaru i zuwa Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba.

Kamerun Präsident Paul Biya Archivbild 30.01.2013

Paul Biya na Kamaru ya ki bai wa Jamhuriyar Afirka ta Tskiya hadin kai

Ko da yake dai daga bisani an shawo kan yajin aikin, amma kuma Kamaru ta yi asarar kudaden shiga daga cikin miliyan dubu 55 da ta saba samu daga jigilar kayayyakin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a kowace shekara. Su ma 'yan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da suka saba zuwa fatauci a kasar ta Kamaru, sai da rikicin tawaye da ake fama da shi yanzu haka ya shafi harkokinsu na kasuwanci, kamar yadda Aboubakar Idris wani mazaunin karamar hukumar Baboua da ke da tazarar kilometa 50 da kan iyakar Kamaru ya shaida min.

Dalilan rashin jituwa tsakanin sassa biyu

Abu na baya-bayan nan da ya tayar da tsumi tsakanin sassa biyu shi ne kashe wani babban jami'in 'yan sandan Kamaru da 'yan tawayen Seleka suka yi. Lamarin da ya sa hukumomin Yaoundé rufe iyakokin kasashen biyu, sai dai daga bisani sun budeshi. Da ma Kamaru ta tari tsohon shugaba Francois Bozize lokacin da 'yan tawayen Seleka da ke rike da mulki suka hambarar da gwamnatinsa. Saboda haka ne farfesa Ouba Ali mai fashin bakin kan al'amuran kasashen biyu, yake ganin cewa har yanzu akwai rini a kaba tsakanin Kamaru da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Zentralafrikanische Republik Vereidigung Michel Djotodia

Michel Djotodia na Afirka ta Tskiya ya kasa shawo kan rikicin tawaye

Rikicin ya yi tasiri a fannin ilimi

Su ma dai daliban Kamaru da ke kan iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun tsinci kansu ciki wani hali na rashin darussa a azuzuwa, sakamakon tsugunar da 'yan gudun hijira da aka yi a makarantunsu. Farfesa Ouba Ali ya ce wannan ya na mayar da hannun agogo baya a yunkurin da kasashen biyu suka yi da farko na raba yaran yankunan da jahilcin da ke addabarsu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal