Dangantaka tsakanin Isra′ila da Amirka | Labarai | DW | 02.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dangantaka tsakanin Isra'ila da Amirka

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya musanta rahotannin da ke nuni da cewa dangantakar da ke tsakanin su da Amirka ta yi tsami.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu

Netanyahu ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi gaban kwamitin hulda tsakanin Amirka da Isra’ila AIPAC gabanin jawabin da yai zi ga majalisar dokokin Amirkan inda ake sa ran zai bukaci majalisar a kan ta dakile duk wani yunkurin cinma yarjejeniya kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran da ake ta takaddama a kai. Ziyarar Netanyahu dai na ci gaba da fuskantar suka kasancewar shugaba Barack Obama bai gayyace shi ba, kana wasu na ganin yana son ya soki huldar Amirka da kasashen ketare a gaban majalisar dokokin kasar. Sai dai ya ce bawai ya je Amirka ne domin ya nuna rashin da a ga Shugaba Obama ko kuma fadar mulki ta White House ba yana matukar girmama su duka, kuma sabanin fahimtar da ke tsakaninsu dangane da batun makamashin nukiliyar Iran din ba zai taba shafar dangantakarsu ba.