Dandalin Matasa: Bunkasar fasahar kwalliya | Zamantakewa | DW | 06.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Dandalin Matasa: Bunkasar fasahar kwalliya

Fasahar kwalliya na dada bunkasa a Najeriya da sauran kasashen gabashin Afirka, inda wasu ke danganta tsarin kwalliyar da al'adu ko addini. To sai dai a zamanin nan ana ganin kwalliyar zamani na neman kwace kwalliyar da.

Africa Fashion Day Berlin 2013 (DW/A. Ilin)

Taron nuna kayan kawa na Afirka a Berlin ya ga halartar 'yan kwalisa a 2013

Fasahar fidda salon kwalliya a Najeriya, na dada samar da ayyukan yi tsakanin matasa maza da mata. A yanzu dai ana ganin tasirin wurare kwalliyar amare da samfurin tufa na fitattun mutane hada da daukar hotunan zamani na ci gaba da samun tagommashi a tsakanin matasa a kasashe da dama. To sai dai ana danganta ci gaban irin na mai hakar rijiya. Inda wasu ke danganta tsarin dinkunan zamani da gurgunta al'adar sa tufa ta malam Bahaushe musamman tsakanin matasa. Amma masu fasahar fidda dinkunan zamani irin MG Gire da ke jihar Adamawa, na cewa duk da ba sa ra'ayin sarrafa dinkunan da ke tsuke kugun matasa ko fidda tsiraicin mata, amma matsin tattalin arziki na tilastasu rufe ido wasu lokuta. Shi kuwa a nashi bangaren, Shamsu Nektarin Bauchi, ya ce hasalima irin dinkunansu na ba da gudumuwar raya sunnah.

Africa Fashion Day Berlin 2013 (Getty Images)

Dinkunan 'yan Afirka sun fara shiga bikin baje koli kayan kawa kamar a nan Berlin 2013

Duk da irin muhawara da neman kare kai da telolin zamani kan yi zargin hannunsu a neman taimakawar bacewar kayan gargajiya na nan daram. Haka nan batu na rashin cika alkawari da ake samun teloli kan yi wani abu ne da ke damun al'umma musamman a irin wannan lokaci na bukukuwan sallah. Sai dai wasu telolin na ganin cewa ba duka aka taru aka zama daya ba.

Matasa masu fasahar sarrafa dinkin zamani na dada samun karbuwa a Najeriya, sai dai ana samun karancin samun damar tallata ayyukan su a kasashen waje. Abin da wasu ke ganin na rage dabarun nuna ayyukan hannu da matasan Najeriya ke yi a idanun duniya. Amma baya ga MG Girei da tuni ayyukansa suka fara tasiri a kasashe kamar Sin da Amirka da Jamus da Faransa harma da Saudiyya, shima Shamsu shafukan sada zumunta na zamani na zama tsanin kai salon dinkunansa zuwa kasashen waje.

Sauti da bidiyo akan labarin