Dan Guinea ya mutu a zanga-zangar adawa | Labarai | DW | 23.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dan Guinea ya mutu a zanga-zangar adawa

Artabu tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaron Guinea ya haddasa mutuwar wani kasar yayin da wasu da dama suka samu raunuka a birane da dama .

Wani dan Guinea daya ya rasa ransa yayin da wasu 'yan kasar da dama suka jikata, a wata arangama da ta gudana tsakanin jami'an tsaro da kuma masu adawa da jadawalin zaben da gwamnati ta tsayar. Tun dai a farkon wannan wata ne jam'iyyun adawa na Guinea suka fara tayar da kayar baya da nufin tilastawa shugaba Alpha Conde shirya zaben kananan hukumomin kafin na shugaban kasa. Sai dai kuma fadar mulki ta Conakry ta ce ba za ta lashe amanta ba.

Rahotannin da ke zuwa mana daga wannan kasa sun nunar da cewa sa-in-sa ta fi kamari ne a garin Labe da ke zama cibiyar madugun 'yan adawan kasar Cellou Dalein Diallo. A Conakry babban birni ma dai, an samu barkewar tashin hankali bayan da 'yan sanda suka hana 'yan adawa gudanar da zanga-zanga. Hakazalika jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen haramta wa madugun 'yan adawa Dalein Diallo fita daga gidansa domin halartar zanga-zangar.