1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan Denmak ne ya kai hari a Copenhagen

Muntaqa AhiwaFebruary 15, 2015

Jami'an tsaron Denmak sun tabbatar da cewa dan asalin kasar mai shekaru 22 ne ya kai harin nan na bírnin Copenhagen, wanda kasar Saudiyya ta yi tir da kaishi.

https://p.dw.com/p/1Ec8u
Hoto: picture-alliance/dpa

'Yan sanda a kasar Denmark sun ce bincikensu ya gano cewa haifaffen kasar mai kuma shekaru 22 a duniya ne ya kai harin birnin Copenhagen a jiya Asabar a lokacin taron fadan albarkacin baki. Suka ce matashin wanda aka kasheshi, wani ne da suka san da shi saboda takadarancinsa. Sai dai basu bada wani karin bayani a kansa ba, hakan nan ma ba su bayyana sunan matashin ba.

Ita kuwa kasar Saudiyya ta yi Allah wadai da harin da aka kai jiya Asabar a Copenhagan inda mutane biyu suka mutu wasu 'yan sanda biyar kuma suka jikkata. Saudiyyar ta ce ba ta ji dadin labaran na Denmark , ganin cewa kai tsaye ya shafi mutane ne da ba su aikata wani laifi ba.

Kasar ta Saudiyya dai na kan gaba wajen hada kai da kasar Amirka dake yaki da kungiyar masu kaifin kishin kafa daular Islama wato IS da ke gwagwarmaya da makamai a Siriya da Iraki da ma wasu kasashe na Larabawa.