1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An cafke maharin da ya tarwatsa bikin 'yanci

Ramatu Garba Baba
July 5, 2022

Jami'an 'yan sandan Amirka sun ce sun yi nasarar kama matashin da ya tarwatsa bikin faretin ranar samun 'yancin kai. Mutum shida sun mutu a sakamakon harin.

https://p.dw.com/p/4Df8h
Chicago: Schüsse bei Parade zum 4. Juli
Hoto: Jim Vondruska/Getty Images

Yan sanda a Amirka sun ce sun yi nasarar kama mutumin da ya bude wuta kan jama'a a lokacin da ake tsakiyar faretin bikin ranar samun 'yancin kai a wani yanki na birnin Chicago. Mutum akalla shida ya hallaka baya ga wasu fiye da talatin da ya raunata.

'Yan sanda sun ce, maharin wani matashi ne mai shekaru ashirin da biyu da haihuwa, kuma ya mika wuya ba tare da wata matsala ba, bayan da aka kwashi sa'o'i ana farautarsa. Harin da aka kai a lokacin bikin da aka saba yi a duk ranar hudu ga watan Yuli na kowacce shekara, ya sanya Amirkawa shiga yanayi na dimuwa.