1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan adawa na Kwango zai yi takaran shugabancin kasa

Suleiman BabayoMay 5, 2016

Bayan tsawon lokaci ana tantanma adawa na Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango Moise Katumbi ya tabbatar zai tsara takara a zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/1IiZJ
Moise Katumbi Chapwe Kongo
Hoto: Getty Images/F. Scoppa

Bayan kwashe watanni ana rade-radi daya daga cikin jiga-jigan 'yan adawa na Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango Moise Katumbi ya tabbatar zai tsara takara a zaben shugaban kasa, yayin zaben watan Nuwamba mai zuwa. Katumbi ya kasance tsohon gwamnan Lardin Gabashin kasar na Katanga, kuma ya ce zai tattauna da jam'iyyu.

Karkashin dokokin kasar Shugaba Joseph Kabila ya kammala wa'adin mulkinsa, amma babu tabbas zai hakura. Tuni ministan sharia na Kongo ya bayyana kaddamar da bincike Katumba da ya ce zai nemi shugabancin kasra bisa dangantaka da kungiyoyin kasashen ketere masu dauke da makamai, abin da ya musanta.