Damuwar duniya a kan rikicin Mozambik | Labarai | DW | 24.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Damuwar duniya a kan rikicin Mozambik

Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna fargaba game da halin da ake ciki a Mozambik, inda 'yan tawaye na RENAMO suka yi barazanar tayar da ƙayar baya.

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin duniya Ban Ki-Moon ya yi kira ga gwamnatin Mozambik da kuma ƙungiyar tawaye ta RENAMO da su kai hankali nesa, tare kuma da zama a kan teburin tattaunawa domin warware rikicin da ke tsakaninsu. Wannan dai ya biyo bayan da barazanar mayar da martani da ƙungiyar Tawayen ta yi bayan da dakarun gwamnati suka kai mata farmaki a tungarta da ke Gorongosa a tsakiyar Mozambik.

Cikin wata sanarwaya Ban Ki-Moon ya nuna damuwarsa game da rikicin da ƙasar ka iya sake samun kanta a ciki, idan sassan biyu na Mozambik da suka daɗe suna gaba da juna suka tsunduma cikin wani sabon faɗa. Shekaru 16 ƙungiyar RENAMO ta shafe ta na gwabza yaƙi da gwamnarin FRELIMO a Mozambik kafin su cimma yarjejeniyar zaman lafiya shekaru 21 da suka gabata.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdourahamane Hassane