1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guinea Bissau: Shirin gudanar da babban zaben shugaban kasa

Abdullahi Tanko Bala RGB
November 22, 2019

Kasar Guinea Bissau da ke yammacin Afirka na shirin gudanar da zabe mai matukar muhimmanci na shugaban kasa a wannan Lahadi mai zuwa, a yayin da ake ci gaba da fama da rikici a tsakanin shugaba da Firaministan kasar.

https://p.dw.com/p/3TY0L
Aristides Gomes und José Mário Vaz Guinea-Bissau
Firaiminista da Shugaban kasar Guinea BissauHoto: Presidency of Guinea Bissau

Sabanin da ake samu a tsakanin Shugaba José Mário Vaz da Firaiminista Aristides Gomes, na neman kassara gudanar da al'amuran gwamnati. jama'a dai na fata zaben shugaban kasar zai kawo masalaha ga wannan dambarwa. Kasar Guinea Bissau ta dade tsawon shekaru tana fama da dambarwar siyasa. Rikici tsakanin 'yan siyasa ya raba kawunan jama'a. Wasu masana dai na ganin batun ba wai na siyasa ne kadai ba, har ma da kokarin juya akalar al'umma da muradun tattalin arziki da kuma hankoron rike madafan iko.

A halin da ake ciki dai yanzu jama'a na cikin fargabar yiwuwar tashin hankali Jens Herpolsheimer masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Leipzig da ke nan Jamus ya ce,  akwai bukatar kasashen duniya su bada gagarumar gudunmawa wajen nasarar zaben da kuma dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Kasancewar kasar na fama da talauci, makarantu da dama har da jami'oi sun rufe, harkokin shari'a da na lafiya sun durkushe yayin da cinikin miyagun kwayoyi ke kara yawaita. Sai dai kuma, ko da an yi nasara zaben ya tafi salin alin, babu tabbas ko sakamakon zai tabbatar da dorewar zaman lafiya inda 'yan takara goma sha biyu kowannensu ke hankoron ganin ya zama shugaban kasa.

BG Präsidentschaftswahlen in Guinea-Bissau
'Yan takara goma sha biyu ne zasu fafata a zabenHoto: Gabriel Fernando Indi

Shugaba Vaz dai na rigima da shugabannin jam'iyyarsa. Tun bayan da ya hau karagar mulki shekaru biyar da suka wuce babu wata kwakkwarar manufa da gwamnatin ta sanya a gaba. A yanzu yana zama shugaba ne na wucin gadi kasancewar wa'adin mulkinsa ya kare tun a watan Yuni. Sai dai dambarwar rikici bayan da ya ce ya kori Firaminista Aristides Gomes a watan Oktoba,  'yan watanni bayan nada shi kan mukamin ya cigaba da haifar da kace-nace.

Guinea-Bissau Wahlen CNE Bissau Felisberta Moura
Hukumar zabe ta shiryawa zaben na wannan LahadinHoto: DW/B. Darame

Kungiyar ECOWAS wadda ta shiga domin sulhunta rikicin, ta nuna goyon bayanta ga Firaministan. Kungiyar tarayyar Afirka da Kungiyar tarayyar Turai da kuma kasashe masu magana da harshen Portuges sun sha shiga tsakani don kawo masalaha ga rikicin. Kungiyar ECOWAS ta ja wa sojojin kasar linzami tare da kara yawan jami'an kiyaye zaman lafiya a kasar tun shekarar 2012 yayin da a hannu guda kuma ta yi barazanar kakabawa kasar takunkumi idan rikicin ya cigaba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani