Dambaruwar sha′anin siyasa a Thailand | Labarai | DW | 28.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dambaruwar sha'anin siyasa a Thailand

Thailand za ta yi manyan zabuka duk da adawar da masu bore ke yi akan hakan.

Gwamnatin kasar Thailand ta sha alwashin gudanar da zabukan kasar a karshen mako, wanda ke cike da cece-kuce, duk kuwa da barazanar da 'yan adawar da ke zanga zanga suka yi na yin kafar ungulu ga zabukan, a kokarin da suke yi na hana jam'iyyar da ke mulki ci gaba da mamaye harkokin mulkin kasar.

Wannan sanarwar dai ta zo ne jim kadan bayan tattaunawar da ta gudana a tsakanin fira ministar kasar Yingluck Shinawatra da kuma jami'an hukumar zaben kasar, wadanda tunda farko suka bukavci jinkirta lokacin zaben, sakamakon rigingimun da suka yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 10, yayin da wasu daruruwa kuma suka sami rauni, a jerin hare hare da harbe harben bindiga da kuma fito na fito a tsakanin ko dai jami'an tsaro da masu boren adawa da gwamnati, ko kuma a tsakanin masu adawa da kuma magoya bayan gwamnatin. Hatta a wannan Talatar (28.01.14) ma, an ji karar harbe harbe a kusa da ginin da fira minista Yingluck Shinawatra, ke yin ganawar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu