Dalilai 10 da za ku so a garin Thuringia
Barka da zuwa Thuringia, jihar Tarayyar Jamus da ba ta yi iyaka da kogi ko kasashen waje ba. Ta zama jihar da mai yiwuwa za a ce, ta fi zama ta tsakiyar Jamus. Tana dai abubuwa da dama na muhalli da tarihi da al'adu.
Erfurt
Duk wanda ya je Thuringia, ya kamata ya ziyarci Erfurt. Daya daga cikin muhimman wurare masu daukar hankali a jihar Thuringia ita ce gadar Krämerbrücke, gada mafi tsawo a nahiyar Turai da ke kewaye da gidaje. Me kuma ya rage da za a gani a Erfurt? Ga kadan daga ciki: Tsakiyar tshohon birnin da Chocin St Mary da kuma wurin ibada mafi tsufa na Yahudawa a Turai.
Goethe
A wannan gidan, daya daga cikin shahararrun marubutan wakoki Jamusawa, ya yi aiki kan bakadamiya kamar "Elective Affinities" ko wasan kwaikwayo na shahararren matsafin Jamus “Faust”. A Weimer za ka iya ziyartar gidan da Johann Wolfgang von Goethe ya zauna tsawon shekaru 50, kafin rasuwarsa a 1832. Ya zauna a gidan tare da matarsa Christiane Vulpius da dansu August.
Schiller
Kana kuma iya ziyartar gidan Friedrich Schiller a Weimar. Marubucin wakokin da iyalinsa sun zauna a nan tsawon shekaru uku. Suna haduwa da Goethe har zuwa lokacin da ya rasu a 1805, yana da shekaru 45. Wadanda ke shaukin samun karin bayani a kan wadannan shahararrun marubuta na duniya, suna iya karanta wasikunsu a taskar ajiyar littafai na Goethe da Schiller da ke Weimar.
Bauhaus
A shekarun 1920 a Weimar aka samar da Bauhaus – wani sabon salon zane da fasahar gine-gine. Tsarin wanda Walter Gropius ya kirkiro, makarantar zane ta Bauhaus na daya daga cikin wadanda suka yi tasiri wajen shata fasalin zane a karni na 20. Gidan adana tarihi na Bauhaus a Weimar, ya bayar da haske ga irin ayyukansu.
Gasasshen nama daga Thuringian
Za ka iya samun wannan cimakar mai dadi a ko ina a Thuringia: Gasasshen naman Thuringia. Za a iya kiransa haka ne kawai, idan a Thuringia aka yi shi. Tsawon lokaci fiye da rabin kayan hadin naman alade da gishiri da barkono da tafarnuwa, ana samun su ne a Thuringia. Ana cin naman da farin burodi.
Dajin Thuringian
Hawa tsauni da doguwar tafiya a kasa – Za ka iya yin dukkan wadannan a dajin Thuringia. Hawan tsanuni mafi shahara a Jamus. Tsaunin Rennsteig, kan dangana da kunyar tsaunuka na dajin Thuringia da ya kai tazarar kafa mita 1,000 kwatankwacin (kafa 3280). Kuma hanyar Rennsteig ita kanta, tana da tsawo: yawancin masu hawa dutsen kan raba tafiyar mai tsawon kilomita 170 zuwa matakai shida.
Gandun dajin Hainich
Godiya ga wurin shakatawa na bakin ruwa da ke dajin, wurin shakatawar na Hainich an saka shi cikin wuraren tarihi na UNESCO. Hanyar tafiyar kafa, na bai wa maziyarta damar jin dadin zuwa wurare da dama a cikin gandun dajin. Maziyartan na ganin saman bishiyoyi da tsawonsu ya kai mita 24 (kafa 78). Wadanda suka yi sa a, su kan ga Jemagu da tsuntsaye da sauran dabbobi da ke rayuwa a dajin.
Wurin Ibada a Wartburg
A 1521, Martin Luther ya fassara littafin Bible na sabon Alkawari daga harshen Girka zuwa Jamusanci cikin makonni 11 kacal yayin da yake wurin Ibada a Warburg, inda ya buya. A matsayin dalibin addini, a karshe ya zama tushen darikar Protestant. An kore shi aka kuma haramta masa dawowa. A 2017 aka cika shekaru 500 da kafuwar Protestant, bikin da aka yi cikin salo a Wartburg.
Bach
Kana iya samun nishadi da wakar Bach, kai kadai ko tare da wasu a wasan da akan yi na tsawon sa a guda. A gidan Bach da ke Eisenach ana iya samun wadannan. An haifi Johann Sebastian Bach a Eisenach a 1685, inda ya zauna shekaru 10. Za kuma ka iya sauraron wakokin shahararren marubucin na duniya a wurare da dama a Thuringia, a lokacin bikin shekara na Bach. Babban bikin wakoki na Thuringia.
Wasan Karta
‘Yan Thuringia suka kirkiro wasan karta na Jamus. Wanda da ake kira Skat, ya samo asali a Altenburg a 1813 bisa tsarin 'yan wasa uku da aka fi sani da Tarot kuma mutum hudu ke yin wasan kartar. Hoton kan sarki. Altenburg nan ne, inda aka fara wasannin a 1509. Har yanzu ana yin kartar kuma ana sayarwa a nan, wanda shi ne tsari mai dacewa daga Thuringia