Dakon sakamakon zaben shugaban kasa a Cote d′Ivoire | Labarai | DW | 26.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakon sakamakon zaben shugaban kasa a Cote d'Ivoire

A Cote d'Ivoire an gudanar da zaben shugaban kasa wanda ake wa kallon zakaran gwajin dafi na dorewar zaman lafiya a kasar bayan kwashe tsahon shekaru tana fuskantar kalubalen rikici.

Shugaba Alassane Ouattara da uwargidansa a yayin kada kuri'a.

Shugaba Alassane Ouattara da uwargidansa a yayin kada kuri'a.

A yayin da yake kada kuri'arsa a Abidjan babban birnin kasar, shugaba mai ci wanda kuma ake kyautata zaton zai lashe zaben da zai bashi damar darewa kan karagar shugabancin kasar a karo na biyu Alassane Ouattara, ya bayyana ranar zaben a matsayin babbar rana ga al'ummar Cote d'Ivoire. Ya kara da cewa ya zamo wajibi a gudanar da zaben cikin lumana da kwanciyar hankali tare kuma da samun hadin kai domin tunkarar kalubalen da ke fuskantar kasar baki daya. A zaben da ya gudana a shekera ta 2010 wanda ya ba wa Ouattara damar darewa kan shugabancin kasar bayan da ya samu nasara akan shugaba mai ci a wancan lokaci Laurent Gbagbo dai, an samu tashin hankali wanda ya yi sanadiyyar barkerwar rikicin bayan zaben da ya janyo asarar rayukan mutane 3,000 tare kuma da raunata wasu da dama baya ga asarar dukiya mai tarin yawa.