1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuwela ta dakile yunkurin juyin mulki

Gazali Abdou Tasawa
June 27, 2019

Gwamnatin Venezuwela ta sanar da dakile wani yinkurin juyin mulki da ta ce kasashen Amirka Kwalambiya da Chili suka shiya yi a kasar, domin hambarar da Shugaba Nicolas Maduro. 

https://p.dw.com/p/3L9ZF
Venezuela Rede von Nicolas Maduro in Caracas
Hoto: AFP/F. Parra

A cikin wata sanarwa da ministan yada labarai na kasar ta Venezuwela Jorge Rodriguez ya fitar, ya ce sun bankado wannan yunkurin juyin mulki wanda aka so a aiwatar da shi a daren Lahadi washe garin Litinin da ta gabata, bayan da jami'an leken asiri na kasar suka yi nasarar kutsawa a asirce a cikin jerin mutanen da suke kitsa juyin mulkin da ma halartar tarukansu. Da yake tsokaci kan wannan batu a gaban tarin magoya bayansa, Shugaba Maduro ya sha alwashin mayar da martani mai tsanani.

"Yace kuna iya kifar da mu ta hanyar da kundin tsarin mulki ya ba ku, amma tun da ku ka zabi hanyar amfani da karfi, to kusan da cewa ba za mu yi maku sassauci ba wajen mayar maku da martani" 

Ministan yada labaran ya ce an kitsa gudanar da juyin mulkin ne tare da wasu sojojin kasar na yanzu da wasu da suka yi ritaya, da kuma tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar da ma wasu manyan 'yan siyasa. Yanzu haka dai an kama mutane shida da ake zargi da hannu a wannan shiri na kifar da gwamnatin ta Maduro.